An Yi Saukar Alkur’ani A Makarantar Sojojin Sama Dake Kano

0
134

JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

A RANAR Asabar 6 ga watan Agusta, makarantar Sojojin sama dake Kano wato “Air force Comprehensive School” (AFCS) ta yi wani kasaitaccen bikin Saukar alkur’ani Mai tsarki wanda aka gudanar a babban zauren taro na makarantar.

Manyan baki da suka hada da iyayen yara daga sassa daban-daban na fadin kasar nan sun halarci bikin inda suka shaida yadda ake koyar da ilimin addinin musulunci da koyar da tarbiyya domin ganin ana samun al’umma tagari kuma wadanda za ayi alfahari dasu a kasa da duniya baki daya.

Shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai ta tarayya Kuma wakilin kananan hukumomin Tudun Wada da Doguwa Alhaji Alhassan Ado Doguwa ya kasance babban bako a wajen taron, ya bayyana cewa ya kasance a wajen wannan biki domin shaida yadda dalibai wannan makaranta suke samun ilimin addini da kuma yadda sashen Islamiyya na makarantar yake bada darussa da kuma tarbiyya ga yara masu tasowa.

Ya ce ” Na taso daga Abuja ne musamman domin in shaida wannan sauka ta alkur’ani mai tsarki kuma in hadu da daliban Makarantar naga yadda suka koyi karatun ganin cewa samun ilimi tun daga tushe abu ne Mai kyau musamman ga yara kanana a wannan lokaci da duniya take tafiya a doron ilimi”. 

Alhaji Alhassan Ado Doguwa ya Kuma hori wadanda suka sauke alkur’ani da suyi amfani da ilimin da ke cikin sa wajen gina kasa da kuma bunkasa tarbiyya a duk inda suka tsinci kansu, tare da yabawa shugaban makarantar Wing Kwamanda M.Garba da daukacin malamai saboda kokarin koyarwa da suke yi ba tare da gajiyawa ba.

Shugaban masu rinjayen ya baiwa dalubai 5 da suka haddace alkur’ani kyautar naira dubu 100 kowannen su, sannan ya bada gudummawar naira miliyan 1 ga kungiyar iyaye da malamai ta makarantar domin gudanar da wasu aiyukan ta.

Tun da farko a jawabin sa, Shugaban makarantar Wing Kwamanda M. Garba ya jaddada cewa makarantar Sojojin sama dake Kano zata ci gaba da bada ingantaccen ilimi da tarbiyya domin ganin kasar nan ta sami al’umma masu basira ta kowane fanni na zamantakewar dan Adam.

Wing Kwamanda M. Garba, ya kuma shaidawa iyaye da manyan bakin da suka halarci bikin cewa sashen Islamiyya na makarantar yana gudanar da irin wannan biki na saukar alkur’ani duk shekara domin kara kwarin gwiwar iyayen yara domin fahimtar yadda ake karatu a makarantar.

A karshe Kwamandan makarantar M. Garba, ya hori daliban da su ci gaba da yin aiki da ilimin da suka damu a Makarantar wajen bada gudummawar su ga ci gaban kasar nan, tare da fatan kowa ya koma gida lafiya.

An gudanar da jawabai da karatun alkur’ani Mai tsarki da rarraba kyaututtuka bisa shaidawar wakilin sarkin Bichi, Nasir Ado Bayero da wakilin kananan hukumomin Tudun Wada da Doguwa a majalisar wakilai ta tarayya da manyan sojoji masu ritaya da wadanda suke aiki da Kuma kungiyoyi dalibai na makarantar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here