Inganta Ilimi: Shugaban Karamar Hukumar Dawakin Tofa Ya Ciri Tuta – Inji Iyayen Dalibai

0
156

JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

IYAYE da masu rike da yara dake yankin karamar hukumar Dawakin Tofa, sun jinjinawa shugaban karamar hukumar Alhaji Ado Tambai Kwa saboda jajircewar da yake yi wajen ganin ilimi yana samun kulawa ta musamman.

A wata ganawa da wakilin mu ya yi da wasu iyaye da masu rike da yara a sassan Karamar hukumar, sun bayyana cewa tun lokacin da shugaba Ado Tambai Kwa ya zamo shugaban karamar hukumar Dawakin Tofa ilimi yake samun kulawa ta kowane fanni.

Alhaji Muhammad Adamu, wani tsohon malamin makarantar kuma mai sharhi kan harkar ilimi, ya jaddada cewa manufofin gwamnatin Alhaji Ado Tambai suna da kyau idan aka dubi da yadda ake cimma nasarar aiwatar da muhimman abubuwa da suka shafi ilimin.

Sannan ya nunar da cewa karamar hukumar Dawakin Tofa, ta zamo abar misali cikin kananan hukumomin Jihar kano wajen kyautata yanayin koyo da koyarwa duk da halin karancin kudden gudanar da harkar ilimi da ake fama da ita a fadin kasa baki daya.

Shima a nasa tsokacin, Malam Ahmed Sani ya nuna matukar jin dadin sa bisa yadda Shugaban karamar hukumar Dawakin Tofa yake kokari dare da rana wajen ganin an cimma nasarar aiwatar da shirin gwamnatin Ganduje na ilimi kyauta Kuma dole kamar yadda ake gani a mazabu 11 dake Karamar hukumar.

Ya ce “iyaye da masu rikon yara ba zasu manta da mulkin shugaba Alhaji Ado Tambai Kwa ba, sannan zasu ci gaba da yi masa addu’oi na samun nasara a harkar mulki da sauran hidimomi na al’umma a duk inda ya sami kansa, inda a karshe ya jaddada cewa iyaye zasu Kara Kokari wajen ganin ilimin da yaran su ke samu ya amfani al’umma cikin yardar Ubangiji.

Wakilin mu ya kuma ziyarci wasu daga cikin makarantu dake Karamar hukumar ta Dawakin Tofa, inda ya ruwaito cewa gudummawar da Karamar hukumar ke bayarwa tana taimakawa wajen zuwan yara da wuri da kuma daukar darasi a cikin yanayi mai kyau duk da halin rashin kudade hannun kananan hukumomin kasar nan.

Haka kuma yadda ake daukar nauyin dalibai da biya masu kudaden makaranta da samar da motocin daukar dalibai musamman mata da kuma yin bibiya kan yadda dalibai dake karatu a manyan makarantu dake fadin kasarnan ya baiwa dalibai damar samun ingantaccen ilimi cikin nasara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here