Wasu Mata Sun Sauya Makasudin Sanya Takunkumin Fuska Bayan Wucewar Cutar Korona

0
167

Daga; Habiba Abdullahi Da Hussaina Bala Kanti, Kaduna

TAKUNKUMIN fuska wato (facemask) wani abu ne wanda masana kimiyar lafiya suka kirkiro shi domin kare kai daga kamuwa daga Cututtuka da a kan iya daukar su ko ta hanyar shakar iska ko numfashi mutane musamman daga marasa lafiya, toh amma bayan bullar cutar Korona, sai al’amarin ya zama na wajibi ga al’umma baki daya a fadin Duniya.

Bayan yanayin da aka yi fama da shi wanda har duniya ta girgiza da wannan al’amarin cutar ta Korona, wasu al’umma musamman mata, sun ci gaba da sanya wannan takunkumin fuska a bisa wasu uzurorin su da wasu biyan bukatu don gujewa wasu abubuwan ko don sauya salon adon su.

A wani binciken da Wakilan Jaridar Gaskiya TaFi Kwabo suka gudanar a garin Kaduna don jin ra’ayoyin wasu al’umma, sun gano cewa a yanzu mafi akasarin mutanen da ke amfani da shi mata ne kuma musamman yan mata domin cimma wani burin dake tattare da su.

Wata budurwa wacce ta buƙaci a sakaya sunan ta, ta bayyana cewa abun da yasa ba ta bar yin amfani da takunkumin ba tun bayan wucewar alhinin cutar shi ne domin jinta ta ke tamkar tana tafiya ne tsirara idan bata saka ba, kana ta kara da cewa ta riga ta saba sanya shi tun lokacin dokar na korona.

Hakazalika, acewar wata budurwa mai suna Aisha Abdullahi, ta bayyana cewa dalilin da yasa ta ke saka takunkumin a yanzu shi ne ne domin ta kare kaita daga kura ko iska idan tana gida ko kan wani abun hawa a hanya.

A nata bayanin, Binta sani, ta bayyana cewa ita ma tana sawa ne bisa ra’ayin ta na kare kanta da yawan kallace-kallace kan hanya, musamman a majalisan yan zaman kashe wando wanda wasu kan yi a cikin unguwani.

Ita kuwa, Salamatu abdulhamid cewa ta yi a yanzu dalilin ta na ci gaba da sanya takunkumin dukda cewa al’umma da dama sun daina amfani da shi a bisa wajibun shi ne, domin ta badda Kama saboda ba kowa ta ke so ya gane ta ba a duk Inda ta je ba.

Hakazalika, Aisha isah ta bayyana ra’ayinta da cewa takunkumin fuskar, ya yi mata riga da wando sakamakon damar da ta ke samu na aikata duk wani abun da take so ba tare da wani yagane fuskar ta da sanin ko ita wace ce ba.

Amina Aliyu kuwa ta bayyana dalilin da cewa tana saka takunkumin a sakamakon cutar asma da ta ke fama da shi wanda hakan yasa ba ta son kura ko jin warin wani abu wanda zai iya daga mata hankali ko tayar mata da ciwon na ta a cikin gida ko a kan hanya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here