Ambaliyar Ruwa A Garin Damaturu Ta Sanya Magidanta Yin Gararamba A Tituna

0
333

Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu.

SAKAMAKON mamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka samu a Damaturu babban birnin jihar Yobe cikin ‘yan kwanakin nan, ya haifar da gidaje da dama sun rushe wadda hakan ya haifar da samun magidanta da iftila’in ya shafa yin Gararamba a kan tituna na neman wurin da za su fake da iyalen su.

Wakilinmu da ya zagaya garin, ya ruwaito cewa an ga wasu daga cikin wadanda bala’in ambaliyar ruwa ya rutsa da su a makale suna neman inda za su ajiye kayansu da sauran matakan gaggawa.

Rahoton ya nuna cewa matsalar ambaliyar ruwa ta zama ruwan dare a duk shekara a wasu Unguwannin garin da suka hada da Pompomari, Sumsumma, Waziri Ibrahim, tsamiyar lilo, Nayinawa, Maisandari da Maduri saboda rashin magudanun ruwa.

A cewar rahoton, ambaliyar ruwan tana shafar dubban jama’a a cikin al’umma, yana mai jaddada cewa babu shekara guda da irin wannan al’ummar ba sa fuskantar irin wannan matsalar.

Da yake zantawa da wakilinmu daya daga cikin mazauna yankin, Malam Ibrahim kare-kare, ya bayyana cewa sun sha yin kira ga gwamnati da sauran hukumomin jin kai da su kawo musu dauki, amma duk da haka babu wani martani daga bangarorin biyu.

A cewarsa, mutane da dama daga cikin al’ummar yankunan ambaliyar ruwan ta tilastawa barin gidajensu, inda ya ce da yawa daga cikinsu na matukar bukatar matsuguni, abinci da sauran kayayyakin agaji.

A cewar al’ummar yankunan Nainawa, Maisandari, Sumsumma da tsamiyar lilo har yanzu suna fuskantar irin wannan kalubale, inda suka yi kira ga gwamnatin jihar Yobe da ta shigo cikin al’amarin ta hanyar gina magudanar ruwa, titina da sauran ababen more rayuwa.

Malam Ibrahim Kare-kare sai dai kuma ya yaba da kokarin Hukumar bada Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe (SEMA) kan yadda take daukar matakan gaggawa a koda yaushe, ya kuma yi kira ga wannan hukumar da ta dauki nauyin kai dauki ga wadanda wannan ambaliyar ta shafa ba tare da wani bata lokaci ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here