An Fara Buga Gasar Cin Kofin Zinariyar Saminaka

0
241

Daga; Isah Ahmed, Jos.

AN fara buga gasar cin Kofin kwallon kafa na zaman lafiya da hadin kai, da Zinariyar Saminaka, Hajiya Munira Suleiman Tanimu, ta sanya a yankin mazabar Lere ta gabas da ke Karamar Hukumar Lere, a Jihar Kaduna, a babban filin wasa na garin Saminaka.

Kungiyoyin kwallon kafa guda 32 ne, da suka fito daga wannan mazaba ta Lere ta gabas da ta kunshi gundumomin Abadawa, Saminaka, Sabon birni da Dan Alhaji, Kayarda da kuma Yar kasuwa ne, zasu fafata a wannan gasa.

Da yake zantawa da wakilinmu, daya daga cikin ‘yan kwamitin shirya wannan gasa, Honarabul Salihu Musa ya bayyana cewa, an sanya wannan kofi na zaman lafiya da hadin kai ne, domin a hada kan matasan wannan yanki, da Karamar Hukumar Lere baki daya.

Ya ce “a wannan gasa, akwai kaututtuka da aka tanadarwa wadanda suka zamo zakaru a gasar.”

“Duk kungiyar da tazo ta daya, za a bata kyautar Naira 200,000 tare da rigunan kwallo da kwallo. Kungiyar da tazo ta biyu, za a bata kyautar Naira 150,000 da rigunan kwallo da kwallo, kungiyar da tazo ta uku kuma, za a bata kyautar Naira 100,000 da rigunan kwallo da kwallo.$

Haka kuma akwai kyauta, ga Dan wasan da yafi cin kwallo a wannan gasa da Alkalin wasan da yafi kokari da kungiyar da tafi da’a da dai sauransu”.

Ya ce “babu shakka wannan gasa, zata yi matukar taimakawa matasan wannan yanki da yan wasan da zasu buga wannan gasa domin ta dalilin wannan gasa, wasu yan wasan, zasu iya fitowa, a dauke su zuwa wasu manyan kungiyoyin kwallon kafa.

Ya yi kira ga matasa, kan su bada goyan baya da hadin kai a wannan gasa da ake gudanarwa, domin a cimma manufar sanya wannan kofi.

A lokacin da aka fara wannan gasa a babban filin wasa na garin Saminaka, Kungiyar kwallon kafa ta Huji Babes daga Yar kasuwa da Kungiyar kwallon kafa ta Buffalo daga Unguwar Tanki ne, suka fafata. Inda aka tashi wasan, Kungiyar Buffalo ta ci jwallo 1, a yayin da Kungiyar Huji Babes, ta tashi ba ko daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here