Zaben 2023: Tsayar Da Yan Takara Nagari Zai Kawo Ci Gaban Kasa – Usman Dan Gwari

0
259

Daga; JABIRU HASSAN, Kano.

AN bayyana cewa idan aka tsayar da yan takara nagari Najeriya za ta sami ci gaba ta kowane fanni sannan dimokuradiyya zata kasance cikin yanayi mai Kya da gamsarwa.

Wannan tsokaci ya fito ne daga Alhaji Usman B. Dan Gwari a zantawar sa da manema labarai a kano dangane da babban zaben Shekara ta 2023 da ake shirin gudanarwa idan Allah ya kai mu.

Usman Dan Gwari ya Kara da cewa a matsayin sa na dan Najeriya wanda yake da damar yin magana kan al’amuran kasa, ya hakikance cewa idan har aka tsayar da yan takara nagari, to ko shakka babu kasar nan zata sami ci gaba ya kowane fanni na zamantakewar al’umma.

Sannan ya nunar da cewa idan aka tsayar da yan takara marasa Kwazo ko shakka babu za a ci gaba da zama cikin yanayi mai cike da kalubale na shugabanci da kuma gazawar shugabannin wajen aiwatar da abubuwa na rayuwa kamar yadda shugabannin ke so.

A karshe, Alhaji Usman yayi Amfani da wannan dama wajen yin godiya ga al’ummar kasar nan saboda bibiyar abubuwa da yake yi musamman a kafafen sadarwa domin kara isar da sakonni da manufofin gwamnati.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here